Labarai

Da dumi dumi ‘yan ta’adda sun kone gidaje sama da saba’in a jihar Zamfara.

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga sun afkawa garin Ruwan Tofa da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da mata da yara 60 a yankin.

An tattaro cewa yan bindigan sun afkawa garin ne a ranar Laraba inda suka kona gidaje da dama, motoci, shaguna tare da lalata kadarorin miliyoyin nairori.
Wani mazaunin garin, wanda ya zanta da sashen Hausa na BBC a ranar Alhamis, ya ce duk sauran mazauna garin sun tsere daga yankin, ya kara da cewa kusan rabin garin sun kone.
Mazaunin, ya ce ba a samu asarar rai ko jikkata ba amma ‘yan bindigar sun harbe daya kuma yana asibiti.

“Sun tafi da mata da yara da yawa. Akwai wani mutum mai mata hudu wanda duk ya dauki matansa ko guda daya ba’a barshi a baya ba. Sun tafi da dangin Hakimin da danginsa, ”inji shi.

Wani wanda lamarin ya rutsa da shi kuma ya ce an dauki kimanin maza, mata da yara 15 daga gidansa, “kuma sun karbe buhunhunan hatsi 90 daga wurina a cikin mota”.

Mun tambayi jami’an tsaro sau biyu amma ba su zo ba sai muka watse daga garin, ”inji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button