Rahotanni

Da dumi dumi ‘yan ta’adda sun sako ‘yan matan Makarantar jangebe da suka sace a Zamfara.

An sako ‘yan matan makarantar sakandaren Gwamnati da aka sace a Jangebe, jihar Zamfara kuma a yanzu haka suna fadar mai martaba sarkin Anka suna jiran jigilar zuwa Gusau, babban birnin jihar.

‘Yan matan da aka sace a ranar Juma’a an yi amannar cewa’ yan ta’addan da suka yi shigar burtu sun yi shigar burtu kamar jami’an tsaro sun dauke su zuwa wani daji.

Wata majiya ta ce an ajiye ‘yan matan a cikin dajin da ke tsakanin Dangulbi da Sabon Birnin Banaga a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Lamarin shi ne kame-kame na karshe da kungiyoyin masu dauke da makamai suka yi a Arewa a makwannin da suka gabata.

Makon da ya gabata, ‘yan ta’addan sun yi awon gaba da dalibai da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara, Jihar Neja.

An saki wadanda aka sace a ranar Asabar.

A watan Disamban da ya gabata ma barayin sun yi garkuwa da yara ‘yan makaranta 300 daga Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara, Jihar Katsina.
Gwamnatin jihar wacce a baya ta nuna kwarin gwiwa cewa ‘yan matan za su dawo ba da daɗewa ba, amma ta ƙi tabbatar ko musanta jita-jitar cewa ta cimma sulhu da masu satar mutanen game da sakin su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button