DA DUMI-DUMI: ‘Yan ta’addar ISWAP sun kai hari hedikwatar ‘yan sandan Najeriya da ke jihar Borno, sun kashe jami’ai hudu.
Majiyar mu ta tabbatar da harin ga SaharaReporters da yammacin ranar Asabar da kuma wani mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafin X (wanda aka fi sani da Twitter) a ranar Asabar.
Bangaren kungiyar Boko Haram da ke samun goyon bayan kungiyar IS mai da’awar kafa daular Musulunci a yammacin Afirka (ISWAP), wanda a da ake kira Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, sun kashe ‘yan sanda akalla hudu a Gajiram da ke Borno. bayan harin da tsakar dare a ofishin ‘yan sanda.
Gajiram na da tazarar kilomita 73 zuwa babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
A cewarsa, ‘yan ta’addan sun yi shigar burtu inda suka kutsa cikin garin a ranar Juma’a da tsakar dare inda suka nufi ofishin ‘yan sanda kai tsaye.
Daga bisani sun bude wuta kan wasu ‘yan sanda inda suka kashe hudu daga cikinsu.
“Majiyoyin sun ce ‘yan sandan a ofishin sun yi artabu da ‘yan ta’addan a wani mummunan artabu da ya hana su kona wuraren,” in ji shi.
“An samu labarin cewa lokacin da sojojin Operation Hadin Kai da ke Gajiram suka kai farmaki wurin, su (‘yan ta’addan) sun gudu.”
Tun bayan rasuwar shugaban JAS, Abubakar Shekau, kungiyar ISWAP ke kara karfafa gwuiwa a yankunan da ke kusa da tafkin Chadi.