DA DUMI-DUMI: Zanga-zangar ta barke a Kano, kan shirin tura sojoji Nijar
Wasu masu zanga-zangar sun bazama kan tituna a jihar Kano domin nuna adawa da amfani da karfi da ake shirin yi don magance rikicin juyin mulkin Nijar.
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta umurci sojojin kasashe mambobin da su kasance cikin shirin ko ta kwana.
A ranar Asabar din da ta gabata ne masu zanga-zangar suka fara zanga-zangar domin nuna rashin jin dadinsu da shirin mamaye jamhuriyar Nijar da sojoji suka yi.
Yayin da suke tafiya cikin jerin gwano suna rera wakar “’yan Najeriya ’yan uwanmu ne, ’yan Nijar ma danginmu ne.
“Nijar tamu ce, ba ma son yaki, yaki da Nijar zalunci ne, makirci ne na sojojin kasashen yamma.”
Sun nuna tutocin Najeriya da Nijar tare da alluna, suna rera taken yaki da yaki.
Hakan ya biyo bayan kiraye-kirayen da bangarori daban-daban suka yi, musamman ’yan Arewa da ke ganin cewa ’yan Nijar makwabta ne da suka yi tarayya da su.