Labarai

Da dumi’dumi: A yau da tsakiyar dare Kungiyar kwadago da ‘yan kasuwa za su fara Yajin aiki a duk fadin Kasar.

Spread the love

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da takwarorinsu na kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa TUC, sun yanke shawarar fara yajin aikin da suka shirya yi a fadin kasar daga tsakar daren yau.

Yajin aikin na zanga-zangar ne domin nuna rashin amincewa da yadda shugaban NLC da wasu suka yi a garin Owerri na jihar Imo a ranar 1 ga watan Nuwamba, da kuma batun ma’aikata da ke kan gaba a jihar Imo.

A ranar 7 ga watan Nuwamba sun yanke shawarar ayyana yajin aikin a fadin kasar nan zuwa ranar Talata 14 ga watan Nuwamba idan ba a biya musu bukatunsu ba.
Ku tuna cewa wasu da ake zargin jami’an gwamnati ne da jami’an tsaro sun kai farmaki kan Ajaero tare da wasu.

Shugabannin kungiyar kwadagon an farfasa motocinsu, inda aka yi musu rauni tare da kwace musu wayoyin hannu, kudi, katin ATM da sauran kayayyaki masu daraja daga shugabannin kungiyar da sauran wadanda suka hallara a sakatariyar kungiyar NLC ta jihar domin fara zanga-zangar da aka shirya yi a ranar 1 ga watan Nuwamba, kan batutuwan da suka shafi kwadago.

Shugaban NLC, da sauran shugabannin NLC na kasa da takwarorinsu na TUC, sun hallara a sakatariyar NLC ta jihar Owerri domin nuna rashin amincewarsu da rashin biyansu albashi da alawus alawus, Fansho, gratuti da kuma rashin bin dokar mafi karancin albashi na kasa.

Hare-haren, cin zarafi da duka da aka yiwa Ajaero da sauran su na ci gaba da haifar da fushi da Allah wadai a fadin kasar da ma sauran kasashen duniya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button