Labarai

Da dumi’dumi: A yau Kaso na Uku daliban Nageriya da suka makale a sudan zasu iso Abuja.

Spread the love

A yau (Asabar) ne ake sa ran kashi na uku na ‘yan Najeriya da suka makale a kasar, wadanda suka kai 132. Zasu iso gida Nageriya.

Kashi na farko na mutane 376 da aka kwashe sun isa Najeriya daga kasar Masar a daren Laraba.

Kashi na biyu na mutane 130 da aka kwashe sun isa kasar daga Port Sudan a ranar Juma’a.

A cewar kakakin hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abdulrahman Balogun, ya ce jirgin na Tarco ya tashi ne da misalin karfe 7:20 na safe agogon Sudan daga Port Sudan tare da ‘yan Najeriya 132; Manya 124 da jarirai takwas.

Balogun ya kuma bayyana cewa “ana sa ran jirgin na sa’o’i bakwai zai isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, Abuja da misalin karfe 1:30-2 na rana.

“Jirgin zai tsaya tsawan awa daya a Juba, Sudan ta Kudu.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button