Labarai

Da dumi’dumi: Abba Gida-Gida Ya nada Sheikh Daurawa daga cikin Kwamitin masu karbar Mulki daga Hannun Ganduje.

Spread the love

A wani Kwamitin karbar Mulki Mai dauke da jaddawalin sunayen mutune sittin da biyar 65 wanda sakataren yada labarai na Zababben gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf Sanusi bature dawakin Tofa ya fitar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa na Daya daga cikin membobin Kwamitin na karbar mulki daga Hannun Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda shine gwamnan jihar Kano Mai ci na yanzu.

Idan Baku manta ba Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shine Shugaban Hukumar Hisba wanda Ganduje ya tsigeshi da nufin al’mundahana da dukiyar Hukumar tare da zargin zubda Darajar Hukumar a idon duniya.

A ranar Ashirin da Tara 29 ga watan mayi ne za’a rantsar da sababbin Zababbun da suka samu Nasarar lashe zaben Gwamnan Dana Shugaban Kasa sanatoci da Yan Majalisar tarayya da Kuma na jiha.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button