Da dumi’dumi: Babban limanin masallacin jihar Zamfara ya yi murabus Sakamakon bidiyon addu’arsa ga Tsohon Gwamna Matawalle ya fita duniya.
Dr Tukur Sani Jangebe, babban limamin masallacin Juma’a na Muslim Foundation da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara ya yi murabus. Ya mika takardar murabus dinsa ne bayan wani faifan bidiyo…
Ya mika takardar murabus dinsa ne bayan wani faifan bidiyo inda aka gan shi yana addu’ar samun nasara ga karamin ministan tsaro kuma tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle ya yi ta yadawa.
Bidiyon dai ya haifar da cece-ku-ce a tsakanin jiga-jigan ‘yan siyasa da mabiya addinai a jihar.
A makon da ya gabata ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben Dauda Lawal a matsayin gwamnan jihar Zamfara tare da ba da umarnin sake gudanar da zaben a kananan hukumomi uku na jihar.
Sai dai a wata wasika da ya aike wa mahukuntan masallacin, Jangebe ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron masallacin da kuma al’ummarsa.
Ya kuma ba da tabbacin goyon bayansa da bayar da gudunmawarsa wajen ci gaba da samun nasarar wannan masallaci da addinin Musulunci a jihar da ma kasa baki daya.
Ya kara da cewa matakin na da nasaba da faifan bidiyo da aka gan shi yana addu’a ga Bello Matawalle.
Ya ce ya yi irin wannan addu’a ga Gwamna mai ci Dauda Lawal a lokacin da yake yakin neman zaben.