Uncategorized

Da dumi’dumi: EFCC ta kama Hadi Sirika.

Spread the love

Hukumar EFCC ta kama Hadi Sirika bisa zargin almubazzaranci da sama da Naira Biliyan 8 da ake alakantawa da badakalar Jirgin Najeriya.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, kan wani bincike da ake yi kan badakalar kudaden da suka kai N8,069,176,864.00.

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama wanda ake zargi ya bayyana a ofishin Hukumar EFCC na Babban Birnin Tarayya da misalin karfe 1:00 na ranar Talata.

A lokacin da Sirika ya isa ofishin hukumar EFCC FCT, a halin yanzu yana fuskantar tambayoyi daga masu binciken EFCC game da badakalar bada kwangilar da ya ba wani kamfani mai suna Engirios Nigeria Limited, mallakin kanin sa Abubakar Sirika.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button