Labarai

Da dumi’dumi: Gwamna Abba Ya Nada Kwankwaso, Shekarau da Ganduje Amatsayin Shugabannin Majalisar dattawan jihar Kano.

Spread the love

Majalisar dattawan Kano da za a kafa a jihar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce.

Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Asabar yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja.

A cewar gwamnan, majalisar za ta yi aiki a matsayin Majalisar ba da shawara ga gwamnatinsa.

SOLACEBASE ta rahoto cewa mambobin majalisar sun hada da gwamnonin da suka gabata da mataimakansu, shuwagabannin majalisar jiha da mataimakansu, shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa (Idan akwai), manyan alkalai masu ritaya, CJN mai ritaya (Idan akwai), Alkalan Kotun Koli mai ritaya, alkalan kotun daukaka kara da suka yi ritaya da kuma masu shari’ar Musulunci shugabanni, da sauransu.

Da wannan ne Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Sanata Ibrahim Shekarau, da Abdullahi Umar Ganduje ke zama mambobin majalisar.

Gwamnan ya jaddada kudirin sa na ci gaba da gudanar da gwamnati a bude take domin tafiyar da kowa da kowa, a sabon yunkurin sa Kanoa sabon Tsarin zamani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button