Labarai

Da dumi’dumi: Gwamna Yahaya Bello na Kogi ya taya Natasha ta jam’iyar PDP murnar samun nasara kotu.

Spread the love

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce ya amince da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tabbatar da Natasha Akpoti-Uduaghan a matsayin zababbiyan ‘yar takarar Sanatan Kogi ta Tsakiya.

Bello na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya taya Akpoti-Uduaghan ta jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da duk wanda ya shiga harkar dimokuradiyya.

Gwamnan ya yi kira ga kowa da kowa a jihar da su amince da matakin.

A ranar Talata ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da Akpoti-Uduaghan a matsayin wanda ta cancanta a zaben Sanatan Kogi ta tsakiya da aka gudanar a farkon watan Fabrairu.

Kotun ta yi watsi da karar da Abubakar Ohere ya shigar saboda rashin cancanta.

A watan Satumba ne kotun sauraron kararrakin zaben jihar Kogi da ke zamanta a Lokoja ta soke nasarar Ohere na APC a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Kogi ta tsakiya.

Kotun ta kuma bayyana Akpoti-Uduaghan a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar dattawa da aka yi a watan Fabrairu.

Sai dai Ohere ya garzaya kotun daukaka kara domin neman hakkinsa amma kotun ta kara tabbatar da Akpoti-Uduaghan a matsayin wanda ya lashe zaben.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button