Labarai

Da dumi’dumi: Gwamnatin jihar Kaduna za ta fara biyan mata masu shayarwa na tsawon watanni shida.

Spread the love

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana aiki tare da majalisar dokokin jihar domin samar da wata doka da za ta ba wa mata masu aiki da shayarwar nono uwa na tsawon watanni shida domin a biya su masu aiki a kamfanoni da masu zaman kansu da na gwamnati.

Jami’ar ciyar da abinci ta hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar, Madam Ramatu Musa ce ta bayyana hakan a yayin wani taron tattaunawa da al’umma da masu ruwa da tsaki tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa mai suna Alive and Thrive a wani bangare na bikin makon shayarwa na duniya.

Masu ruwa da tsaki a dandalin sun jaddada muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zalla domin magance matsalar rashin abinci mai gina jiki da ke addabar yara tare da rage mace-macen yara a jihar.

Kididdiga daga hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Kaduna ta nuna cewa kashi 41.1 cikin 100 na yara ne kawai ake shayar da su nonon uwa zalla, yayin da hudu daga cikin yara goma ke shayar da nonon uwa na tsawon watanni shida ko sama da haka.

Hakazalika, Cibiyar Kiwon Lafiyar Abinci ta Kasa, (NNHS) ta shekarar 2015 ta tabbatar da cewa kashi 42 cikin 100 na yara a Jihar Kaduna ana rasa su daga rashin abinci mai gina jiki yayin da kashi 52.1 cikin 100 na yara ‘yan kasa da shekaru biyar suke rashin abinci mai gina jiki.

Domin warware wannan gibin, gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa mai suna Alive and Thrive, sun shirya taron tattaunawa da al’umma da masu ruwa da tsaki a sassan kiwon lafiya domin wayar da kan su kan muhimmancin shayar da yara nonon uwa zalla.

Taron wanda ke da taken: “‘Ba da damar shayarwa: samar da canji ga iyaye mata masu aiki”, da nufin yin hulɗa tare da daidaikun mutane da cibiyoyi da fahimtar ƙalubalen wurin aiki ga iyaye mata masu aiki da ci gaba.

Daga cikin wasu manufofin, wannan shiri na masu ruwa da tsaki kan shayar da jarirai, ana sa ran za su nemi alƙawura daga cibiyoyi don ba da kariya, ingantawa da tallafa wa iyaye mata masu aiki don shayar da ƴaƴan su nonon uwa kawai a cikin yanayi mai daɗi na akalla watanni shida daga ranar haihuwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button