Da dumi’dumi: Gwamnatin Tinubu ta Amince da kashe biliyan 5.9bn domin haska fitilu a titin Jirgin Kasan Abuja.
Majalisar zartaswa ta tarayya, a yau ranar Litinin, ta amince da kashe Naira biliyan 5.9 don gina hanyoyi da Samar da fitilu da za a yi amfani da layin dogo titin Jirgin Kasa na Abuja.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar yayin da yake bayyana sakamakon zaman majalisar da aka yi a makon nan karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu Aso Rock Villa, Abuja.
Wike ya bayyana cewa, shugaban kasar ya sanya lokacin kammala aikin jirgin kasa na Abuja, inda ya jaddada mahimmancin shirya hanyoyin da za a bi zuwa tashar jirgin kasa.
Ya ce “a yau majalisar ta amince da bayar da kwangilar gina titunan jirgin kasa na Abuja. Kuna sane cewa Shugaban kasa ya ba da umarnin cewa yana son hawa kan tsarin layin metro.