Labarai

Da dumi’dumi: Jam’iyar LP ta Peter Obi ta rasa kujerun ‘yan Majalisar tarayya biyu Sakamakon hukuncin Kotun zabe

Spread the love

Kotun sauraren kararrakin zabe ta kasa da ke zama a Umuahia, Abia, ta kori dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Arochukwu/Ohafia, Ibe Okwara, na jam’iyyar Labour Party (LP).

Ta bayyana Dan Okeke na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar dokokin tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 a mazabar.

Yayin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana dan takarar jam’iyyar LP a matsayin wanda ya lashe zaben, Okeke da bai gamsu ba ya garzaya kotu domin neman a soke zaben Ibe.

Ya yi zargin cewa nasarar da dan takarar LP ya samu bai bi ka’idojin doka ba.

Watanni bayan karar da ya shigar, kwamitin mutum uku karkashin jagorancin shugabanta Justice Adeyinka Aderegbegbe ya bayar da ba asin sa tare da yanke hukuncin cewa zaben Ibe bai bi ka’idojin dokar zabe ba.

Daga nan ne ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben sannan ta umarci INEC da ta janye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Ibe sannan ta ba Okeke sabo.

Hakazalika, wata kotun sauraron kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ke zama a Umuahia ta kori dan majalisa mai wakiltar mazabar Abia ta Arewa/Kudu a majalisar wakilai Emeka Nnamani na jam’iyyar Labour Party (LP).

Kotun mutum uku ta bayyana Alex Ikwechegh na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaben.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button