Labarai
Da dumi’dumi: Kawo Yanzu Fursunoni tare da Yan Boko Haram 274 sun bace daga gidan yarin Maiduguri – NCoS
Hukumar Kula da Gidan Yari ta Najeriya (NCoS) kawo yanzu ta bayyana cewa fursunoni 274 ne suka bace bayan ambaliyar ruwa ta ruguje katangar Cibiyar Tsaro ta Matsakaicin gidan Yarin (MSCC) Maiduguri.
Kakakin NCoS, Umar Abubakar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Lahadi.
Ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri a jihar Borno a baya-bayan nan ta yi barna.
Ambaliyar ruwan wadda ta rugujewar dam din Alau bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, ya mamaye manyan sassan birnin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da miliyan guda tare da yin sanadiyar mutuwar mutane akalla 30.