Labarai

Da dumi’dumi: Kotu ta Kori karar da Jam’iyar NNPP ta shigar akan Gwamna Caleb na jihar Plateau

Spread the love

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke zamanta a Jos, Jihar Filato ta yi watsi da karar da Alfred Dabwan, na jam’iyyar NNPP ya kai Caleb Mutfwang, na jam’iyyar PDP tare da Cin tarar Naira miliyan 1.5 kan wanda ya shigar da karar.

Dabwan ya nemi a soke zaben ranar 18 ga Maris, 2023 wanda Mutfwang ya yi nasara a kan abin da ya kira cire logon jam’iyyar NNPP da INEC ta yi ba bisa ka’ida ba.

A wani labarin kuma, kotun sauraron kararrakin zabe ta kasa a ranar Litinin ta kori Peter Gyendeng na jam’iyyar PDP a matsayin mamba mai wakiltar mazabar Barkin-Ladi/Riyom na tarayya tare da bayyana Fom Chollom na jam’iyyar LP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Fom ya kalubalanci ayyana Gyendeng na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da INEC ta yi a kan cewa Gyendeng ba a tantance shi a matsayin Dan Jam’iyyar PDP ba a lokacin zaben saboda PDP ba ta da ingantaccen tsarin Dan takara a lokacin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button