Labarai
Da dumi’dumi: Kotun ECOWAS ta ba da umarni ga sojojin mulkin Niger kan gaggauta sakin shugaban Bazoum.

Kotun ECOWAS ta bukaci a gaggauta sakin hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum.
Bazoum, wanda aka hambarar da Gwamnatin sa a juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli, yana ci gaba da tsare tun daga lokacin.
Kotun ECOWAS ta bayar da wannan umarni ne a ranar Juma’a a Abuja, babban birnin Najeriya. Ta ce ci gaba da tsare shi ba bisa ka’ida ba ne kuma ta dage da “sakinsa nan take ba tare da wani sharadi ba”.
A halin da ake ciki kuma, hukumar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS/CEDEAO, ta dakatar da Jamhuriyar Nijar a hukumance daga dukkan sassan yankunan kasar, har sai an maido da tsarin mulkin Dimokuradiyya a kasar.