Da dumi’dumi: Ku yi Adalci ku bayyana Sakamakon da Al’umma suka zaba a jihar Taraba ~Sakon Kwankwaso ga Hukumar zabe.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yayi kira ga Al’ummar jihar Taraba da su cigaba da kwantar da hankalinsu tare da zaman lafiya da bin doka da Oda Hakan na kunshe a cikin wani bidiyon da mataimakinsa kan harkokin Sada zumintar zamani Hon Saifullahi Hassan ya wallafa Kwankwaso Yana Mai cewa.
Yan uwana Yan jihar Taraba musamman ya Yan jam’iyar NNPP Ku cigaba da kwantar da hankali Kuma ku guji duk wani Abu da zai jawo Tashin hankali anan nake kira ga Jami’an tsaro da duk hukumomin da ya shafa a tabbatar da anyi abinda ya dace na bin ka’ida tare da bayyana Sakamakon da Al’umma suka zaba bisa Adalci.
Kwankwaso na wannan magana ne a daidai lokacin da Prof Sani Yahaya na jam’iyarsa ya NNPP ke kan gaba da kuri’u masu Tarin yawa lamarin da ya rage Kananan hukumomi hu’du kafin a bayyana Sakamakon zaben karshe na Jihar.