Labarai

Da dumi’dumi: Kungiyoyin Arewa sun Ya bawa Gwamnatin Shugaba Tinubu kan gyara Matatar man fatakwal

Spread the love

Kungiyoyin Arewa – Arewa Youth Consultative Forum da Northern Awareness Network, sun yabawa Gwamnatin Tarayya da Kamfanin Man Fetur na Najeriya Ltd bisa sake farfado da matatar man Fatakwal.

Matatar man da aka girka tana iya hako ganga 60,000 a kowace rana, ana sa ran za ta rage dogaron da Najeriya ke yi man fetur da ake shigowa da su daga kasashen waje, da kara karfin tattalin arziki da kuma taimakawa wajen daidaita farashin mai.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar AYCF, Yerima Shettima ya fitar ranar Talata a Kaduna, ya yabawa gwamnatin tarayya da hukumar NNPC bisa kokarin da suke yi na farfado da matatar man.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button