Da dumi’dumi: Kwamitin zartawar NNPP sun Kori Kwankwaso kwata kwata daga jam’iyar.


Kwamitin zartaswa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta kori Sanata Rabi’u Kwankwaso, sakamakon kin bayyana gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya tuna cewa tun da farko shugabannin jam’iyyar sun dakatar da Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP a 2023 a wani taron su a ranar 29 ga watan Agusta a Legas.
Kuna ita tunawa cewa Majalisar Zartawar jam’iyar (NEC) ta NNPP ta kafa kwamitin ladabtarwa ta kuma umurce ta da ta gayyaci Kwankwaso domin ya kare zarge-zargen cin hanci da rashawa na jam’iyya da kuma karkatar da kudaden jam’iyya/kamfen cikin kwanaki biyar.
Hukumar zaben ta yi gargadin cewa rashin bayyana gaban kwamitin ladabtarwa, za a kori Kwankwaso daga jam’iyyar kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar 2022 ya tanada.
Sakamakon haka, Mista Abdulsalam Abdulrasaq, mukaddashin Sakataren Yada Labarai na NNPP, a wata sanarwa da ya fitar a yau ranar Talata a Legas, ya ce Kwamitin ya kori Kwankwaso ba tare da bata lokaci ba saboda ya ki amincewa da gayyatar kwamitin.
Abdulrasaq ya ce: Kwamitin ya yi zaman gaggawa a ranar Juma’a, 1 ga Satumba, inda ta warware kamar haka.
“Bayan kin bayyana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a gaban kwamitin ladabtarwa da ya zauna a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta bayan an gayyace shi a rubuce, an kore shi daga NNPP nan take.
“Za a kai rahoton tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa wuraren da suka dace domin amsa tambayoyi kan rashin kudi da suka shafi almubazzaranci da dukiyar al’umma.”
NAN ta ruwaito cewa rikicin cikin jam’iyyar NNPP ya faro ne lokacin da NWC na jam’iyyar da ke biyayya ga Kwankwaso, ta sanar da dakatar da wanda ya kafa NNPP, Dokta Boniface Aniebonam da sakataren yada labarai na kasa, Dr Agbo Major a ranar 24 ga watan Agusta.
NAN