Labarai
Da dumi’dumi: Kwankwaso yace Abba zai warware matsalar masarautun kano da aka raba su gida biyar.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a wani bidiyo Dake yawo an hango shi Yana cewa Batun Sarautar Kano ai matsalar bata maganar cire sarki bane ko a.a ai matsalar tana da yawa har da batun matsalar karkasa sarautar kashi-kashi zuwa gida 5, sai dai zamuyi nazari kuma shi wannan sabon Gwamnan Allah zai bashi hikima ta yadda zai zo ya warware matsalar; inji Kwankwaso
Ana ta tattaunawa tare da Cece kuce kan Sarautar Jihar Kano tun bayan da Engr Abba Kabir Yusuf ya lashe zaben Gwamnan jihar Kano Aminu Ado bayero ne sarkin Cikin Garin Kano wanda gwamna Ganduje ya nada bayan na tsige Muhammadu Sanusi Na II daga Sarautar ta Kano