Labarai

Da dumi’dumi: Majalisar dattijai ta dakatar da Abdul Ningi Majalisar ta Kuma Aike da takardar gargadi ga Sanata Kawu Sumaila.

Spread the love

Majalisar dattijai ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku saboda zargin da ya kawo na cewa majalisar ta amince da kasafin kudin 2024 guda biyu.

A yau ranar Talata ne aka dakatar da shi a zauren majalisar dattawa.

A yau ranar Talata ne dai majalisar ta tuhumi Dan majalisar dattijai sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, Sanata Abdul Ningi.

Wani mamba a kwamitin kasafin kudi a majalisar dattijai, Jimoh Ibrahim, ya gabatar da kudirin dakatar da Ningi na tsawon watanni 12 bisa zargin tayar da hanka wanda ka iya kawo rashin samun zaman lafiya a majalisar dokokin kasar da kuma kasar ta hanyar tsawaitawa.

Ibrahim mai wakiltar mazabar Ondo ta Kudu, ya kuma bukaci majalisar dattijai ta aike da takardar gargadi ga Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu Suleiman Kawu kan yada labaran da ake yadawa a shafukan sada zumunta, sannan ya bukaci shi (Kawu) ya ba da hakuri.

Nan take abokin aikin sa mai wakiltar Delta ta tsakiya, Sanata Ede Dafinone ya goyi bayan kudirin Sanatan na Ondo.

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ne ya sanar da kudirin a zauren majalisar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button