Labarai

Da dumi’dumi: Majalisar Dunkin duniya ta zabi jihar Kano domin bawa dalibai sama da mutun milyan daya Ilimin fasahar zamani.

Spread the love

An zabi jihar Kano a matsayin daya daga cikin jihohin da zasu samu tallafin Ilimi na kasashen da suka ci gajiyar sabon shirin samar da ilimi da karfafawa kungiyar Tarayyar Turai tallafi a Najeriya.

Shirin na da nufin kara yawan ‘yan mata da maza da ke cin gajiyar damammakin koyo da fasaha masu inganci a jihohin Kano, Jigawa da Sokoto.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta fitar kuma ya rabawa manema labarai a ranar Talata.

Shugaban tawagar asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, Mista Michael Banda, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Doguwa game da shirin a ofishinsa a ranar Talata.

Ya ce shirin na shekaru hudu wanda ya fara daga Satumba 2023 zuwa Agusta 2027 zai kunshi kananan hukumomi 10 kowace daga jihohin Kano, Jigawa da Sokoto.

“Shirin an yi shi ne don amfanar kimanin dalibai miliyan 1.2, malamai 5,000, jami’an ilimi 150 da kuma al’umma 5,400 a fannoni daban-daban na harkar ilimi.

Aikin shirin ya kasu kashi uku manya-manyan abubuwan da suka hada da karfafa tsarin mulki da ilmantarwa, fadada hanyoyin samun lafiya da yanayin ilmantarwa tare da ba da inganci, ci gaba da koyo da ingantattun kwarewa,” in ji shi.

Abinda ya lura cewa yayin da duniya ke canzawa ta hanyar fasahar dijital, akwai buƙatar ɗaukar tsari mai tsauri ga fannin ilimi ta yadda za a bai wa malamai da ɗalibai horo na dijital.

Ya kuma yi nuni da cewa, idan har ana son bullo da fasahar zamani don kawo sauyi a fannin ilimi, to lallai ne malamai da dalibai da jami’an ma’aikatar su ba da himma sosai wajen samun horon da ake bukata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button