Labarai

Da dumi’dumi Majalisar tarayyar Nageriya na so a Kara Albashin malaman Sakandiri Zuwa dubu Dari biyar biyar N500,000.

Spread the love

Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ilimin Jami’o’i Abubakar Fulata Ya yi kira da a kara albashi ga malaman Firamare, Sakandare da Jami’o’i.

Shugaban ya ce ya kamata ya Yanzu malaman firamare su rika karbar Naira 250,000, Sakandire N500,000 da kuma Naira miliyan 1 ga malaman jami’o’i a duk wata.

Mista Fulata yana magana ne a wajen wani taron bita na kwana daya na masu ruwa da tsaki na kasa kan bunkasa taswirorin tsarin ilimi na Najeriya (2023-2027), a Abuja a yau Alhamis.

Fulata ya ce yana da kyau malaman Najeriya su kara kwarin gwiwa ta hanyar biyan su kudaden da suka dace domin koyar da yara.

Ya kuma jaddada wajibcin fassara dukkan litattafan darussa zuwa harsunan cikin gida domin kamo matakin tsarin na duniya.

A cewarsa, gwamnatocin da suka shude sun yi kokari a fannin ilimin kasar amma hakan bai haifar da sakamakon da ake so ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button