Labarai

Da dumi’dumi: Matasan Arewa sun yi barazanar fara zanga-zanga kan dauke CBN da FAAN zuwa jihar Legas

Spread the love

Kungiyar masu rajin tabbatar da dimokaradiyya ta arewa, hadin gwiwar matasan Arewa, ta ki amincewa da mayar da wasu muhimman sassan babban bankin Najeriya da kuma hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama na Najeriya zuwa Legas da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi.

Kungiyar da ta kunshi kungiyoyin farar hula 16 a yankin Arewa, irinsu Arewa Defence League, Association of Northern Nigeria Students, Arewa Youth for Development and National Unity Advocate Council, Arewa Young Women Rights Advocate Council, Arewa Youth in Defence of Democracy, Arewa Radio da sauransu. Masu sharhi a Talabijin, da sauransu, sun yi gargadi game da matakin.

A cewar gamayyar kungiyoyin, gazawar da gwamnatin shugaba Tinubu ke jagoranta na janye wannan mataki zai sa su hada kai da matasa a fadin jihohin Arewa 19 domin daukar matakin da ya dace kan gwamnatin.

A kwanakin baya ne dai CBN ya sanar da sauya wasu sassan zuwa Legas, sakamakon cunkoso a babban ofishin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button