Labarai

Da dumi’dumi: Matatar man fetir na Dangote za ta fara tace danyen mai ganga dubu 350,000 a ko wacce rana.

Spread the love

Shugaba Babban Jami’in Kamfanin Dangote Group, Aliko Dangote, ya ce matatar Dangote da ke Lekki, Legas za ta fara aikin tace danyen mai ganga 350,000 a kowace rana.

Dangote, wanda ya bayyana hakan yayin wata hira da jaridar Financial Times, ya kuma bayyana cewa matatar za ta samar da kusan ganga miliyan shida na danyen mai a watan Disambar 2023.

Zamu fara da ganga 350,000 a ko wacce rana,” Dangote ya shaida wa Financial Times, ya kara da cewa an riga an kulla yarjejeniya kan “kayan farko na kimanin ganga miliyan 6” don jigilar kaya a wata mai zuwa.

Dangote ya ce ya yi imanin cewa matatar man za ta iya kaiwa Yana Samar sa ganga 650,000 a rana a karshen shekarar 2024, duk da cewa IMF ta ce tana shakkar za ta kai fiye da kashi uku cikin uku na hakan nan da shekarar 2025.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button