Da dumi’dumi: Muhyi yasha alwashin kwato ku’din tallafin noma bilyan hu’du 4bn da suka bata a Gwamnatin Ganduje.
Hukumar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta ce ta fara gudanar da binciken sama da Naira biliyan 4 da kudaden gwamnati da suka bata daga kamfanin samar da noma na jihar Kano (KASCO).
Shugaban hukumar Muhyi Rimingado ya tabbatar da haka a lokacin da ya jagoranci wani rangadin bincike a rumfunan ajiye kayayyakin da ake zargin motoci da manyan tarakta da taraktoci da ake kyautata zaton an sayo ne da kudaden da aka zabo a karamar hukumar Kumbotso. .
Mista Rimingado ya ce an karkatar da kudaden ne daga KASCO zuwa wata kungiya mai rijista da Hukumar Kula da Kamfanoni, mai suna Association of Compassionate Friends.
“An yi nufin kungiyar ne don inganta tare da kula da rayuwar ‘ya’yan marasa galihu a cikin al’umma, amma abin takaici, an mayar da ita wata na’ura mai satar dukiyar jama’a,” in ji shi.
Shugaban ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano na ciro wadannan kudade ne a matsayin tallafi ga hukumar KASCO amma an zaftare su ne ta hanyar amfani da kungiyar masu rijista da wani kamfani mai suna ‘company of limestone’.
“Mun kama mutane takwas da ake zargi da bayyana sahihan bayanai ga hukumar.
“Daya daga cikin su ya ce an ba shi wasu kudi ne don ya yi karya a KASCO, amma ya ajiye kudin a gefe yana jiran wani lokaci kamar haka, kuma da radin kansa ya mayar da kudin.
“Ya zuwa yanzu, mun kwato Naira miliyan 15 kuma mun yi nasarar dakile kusan Naira miliyan 8,” in ji shi.
Mista Rimingado ya ce hukumar na da shakkun yadda ake yin wasu hada-hadar kasuwanci tsakanin kamfanonin da wasu bankuna, yana mai jaddada cewa za a iya gayyatar wasu manajojin bankin domin warware wasu batutuwa.