Labarai

Da dumi’dumi: Rundunar sojojin ECOWAS suna taro a Abuja domin kawar da sojojin Kasa Niger tare da dawo da tsarin Dimokuradiyya.

Spread the love

Bayan juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar da wa’adin kwanaki bakwai da aka baiwa shugabanin na su saki shugaba Bazoum da ake tsare da shi kan karagar mulki su yi murabus, hafsan hafsoshin tsaron yankin yammacin Afirka sun fara wata muhimmiyar ganawa a hedkwatar tsaro tare da babban hafsan tsaron Najeriya a Ma’aikatan, Janar Christopher Musa ne ya jagoranci taron.

Ana sa ran taron kungiyar ECOWAS zai shafe kwanaki biyu ana yi.

Idan dai za a iya tunawa a ranar Lahadin da ta gabata ne shugabannin kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma suka kakaba wa Nijar takunkumi tare da fitar da gargadi kan yuwuwar yin amfani da karfin soji kan mulkin soja bayan wa’adin mako guda na dawo da shugaba Mohamed Bazoum.

Hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Ghana, Gambia, Togo, Saliyo, Laberiya, Cote d Ivoire, Cape Verde, Senegal, Jamhuriyar Benin, Guinea Bissau.

Wakilan kasashen Nijar da Guinea da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea-Bissau ba su halarci taron ba

Haka kuma akwai kwamishinan harkokin siyasa na kungiyar ECOWAS.

A nasu bangaren, tun da farko dai gwamnatin sojan kasar ta bayyana rashin amincewarta da duk wani hari da kasashen yankin ko na yammacin duniya ke kaiwa Nijar.

Sanarwar da kungiyar ta ECOWAS ta fitar bayan taron kolin shugabannin yankin ya ayyana “ba za ta jure ba” game da juyin mulki inda ta kara da cewa “zata dauki dukkan matakan da suka dace don maido da tsarin mulki” idan ba a biya bukatunta cikin mako guda ba.

Wannan dai shi ne karon farko da kungiyar ECOWAS ta yi barazanar daukar matakin soji domin dakile juyin mulkin da aka yi a yankin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button