Da dumi’dumi: Rundunar ‘Yan sanda ta nada AIG Ari Amatsayin Mataimakin Sufeton ‘yan sanda Mai kula da shiyyar Arewa ta tsakiya.
Hukumar kula da ‘yan sanda ta kasa (PSC) ta sanar da nadin mataimakin sufeto-Janar na ‘yan sanda (AIG) Ari Mohammed Ali a matsayin sabon mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda (DIG). Ya maye gurbin DIG Ade Ayuba, wanda kwanan nan ya yi ritaya daga aiki. AIG Ali, wanda a baya shine mai kula da shiyya ta daya a Kano.
Ari Wanda ya fito ne daga jihar Nasarawa a shiyyar Arewa ta tsakiya ya ci gaba da wakilcin yankin da Ayuba ke rike da shi a baya
Sanarwar Hukumar wacce ta fito a cikin wata sanarwa da shugaban yada labarai da huldar jama’a na PSC Ikechukwu Ani ya fitar, ta kuma hada da sakon taya murna ga DIG Ari Mohammed Ali. Argungu ya bukaci sabon DIG da ya yi iya kokarinsa wajen yi wa kasa hidima.
Ga Tarihin AiG Ari a Takaice,
An haifi CP Ari Muhammed Ali a ranar 1 ga Maris 1965 ga iyalan Mista da Misis Ali. Ya fito ne daga karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa. Ya yi Digiri na farko na Kimiyya a Laburare da Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Maiduguri a 1987, ya Kuma karanci Kimiyya a Harkokin Masana’antu daga Jami’ar Jihar Delta, Abraka a 2000. Ya kuma yi Diploma a Kimiyyar ‘Yan Sanda a sashen gida na Burtaniya, a kwalejin ‘yan sanda Jos a 2009. CP yana da digiri na uku a fannin masana’antu daga Makarantar Kasuwancin Jami’ar Irish a Penbroke Square United Kingdom a 2011.
Ya shiga aikin ‘yan sandan Najeriya a matsayin jami’in ‘yan sanda ASP course 16 a ranar 3 ga Maris 1990. Ya halarci makarantar ‘yan sanda ta Kaduna, bayan da ya kammala horon academy, sai aka tura shi rundunar ‘yan sandan jihar Delta a matsayin mataimakin Sufirtandan ‘yan sanda a Nuwamba 1991.
Ya yi ayyuka da dama a aikin ‘yan sanda kamar haka; Ya yi aiki a matsayin Dibisional Police Officer ‘B’ Dibision Asaba a shekara ta 2001. CP an tura shi rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa a shekara ta 2002 inda ya yi aiki a matsayin jami’in ‘yan sanda Dibision Ekeki Dibision a Yenagoa kuma a waccan shekarar aka tura shi ofishin rundunar jihar Legas. .
AiG ya yi aiki a matsayin Dibisional Police Officer Denton Police Station, Ebute metta a shekarar 2003, DPO Apapa a shekarar 2005, Area Commander Area ‘C’ Surulere Jihar Legas a shekarar 2011, Area Commander Area ‘B’ Apapa a shekara. 2012. Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyukan jihar Rivers a shekarar 2014. CP ya kuma yi aiki a kwalejin ‘yan sanda ta Jos a matsayin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da kwasa-kwasai a shekarar 2016,
mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da shiyyar. CID Zone 7 Abuja a shekarar 2017, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da harkokin mulki Makurdi, jihar Benue. Ya kuma kasance mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da aikin ‘yan sandan jihar Legas inda ya yi aiki na tsawon shekaru 3 kuma a wannan lokacin an rage yawan aikata laifuka zuwa kasa sosai a jihar Legas.
An kara masa girma zuwa mukamin kwamishinan ‘yan sanda ne a ranar 18 ga watan Disamba 2020. ya zama kwamishinan ‘yan sandan jihar Delta na 20 daga nan ya zama AIG Mai kula da shiyyar lagos ta biyu da Kuma Kano shiyya ta Daya sai Yanzu da ya zama Mataimakin Shugaban Rundunar ‘Yan sanda Mai kula da shiyyar Arewa ta tsakiya.