Labarai

Da dumi’dumi: Sani Liman Kila Kwanturola Immigration na Jihar Kano yayi murabus.

Spread the love

Rahotonni Dake shigowa na cewa Sani Liman Kila Shugaban Rundunar Jami’an kula da shige da fice na Kasa reshen Jihar Kano ya ajiye aikin sa a jiya talata.

Kafin sani Liman Kila ya ajiye aiki ya kasance jami’i ne na Hukumar kula da shige da fice na sama da shekaru talatin wanda harya Kai ga samun mukamin kwanturola na hukamar ya Kuma rike mukamai da dama a cikin Hukumar wanda suka ha’da…

Mataimaki na musamman ga Shugaban Rundunar shige da fice na Kasa (Comptroller Of Immigration) daga watan Satumba na shekara ta 2020 zuwa watan Maris na 2021.

Ya rike Jami’in Kula da Fasfo a Amana City Dawakin Kudu dake Kano daga watan Maris na shekara ta 2021 zuwa watan Augusta 2022

Shugaban Hukumar Kula da shige da fice na reshen Jihar Kaduna daga watan Agusta 2022 zuwa Fabrairu 2022.

Shugaban Hukumar Shige da Fice na rashen Jihar Kano daga watan Fabrairu 2023 zuwa watan Mayu na 2023.

Ra’dera’di daga Bakin Al’ummar Gari na cewa ajiye aikin na sani Kila na da Nasaba da lashe zaben Sanata Uba sani amatsayin sabon gwamnan jihar Kaduna duba da alakar dake tsakanin su da sanatan wasu ma na cewa Liman Kila shine ake zaton ka iya zama Shugaban ma’aikata na Zababben gwamnan ta jihar Kaduna kasancewarsa mai Gaskiya da rikon Amana kamar yadda na kusa dashi suka bayyana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button