Labarai

Da dumi’dumi: Shugaba Tinubu ya amince da a rabawa jihohin bilyan biyar-biyar 5bn domin rage ra’a’din cire tallafin man fetir ga talakawa.

Spread the love

Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa, NEC, a yau ranar Alhamis ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta amince da bayar da tallafin Naira biliyan 5 ga kowace jiha daga cikin jihohi 36 na tarayyar kasar nan domin siyan hatsi da kuma tirela na shinkafa guda biyar ga kowace jiha a matsayin tallafin rage radadi. sakamakon cire tallafin man fetur.

Majalisar ta kuma amince da raba buhunan masara 40,000 da za a raba wa jihohi.

Har ila yau, ta umarci hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, da ta raba kayan abinci ga jihohin da ke kan iyaka da jamhuriyar Nijar, sakamakon tabarbarewar siyasa a kasar.

Wasu daga cikin sakamakon taron NEC da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa a Villa Abuja.

Da yake zantawa da manema labarai a karshen taron, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, ya ce amincewa da Naira biliyan 5 da manyan motocin shinkafa da hatsi na daga cikin matakan kawo mafita na wucin gadi ga tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin, domin gwamnati ta ci gaba da aiki tare da ƙarin shirye-shirye masu dorewa.

Ya ce jihohin za su sayi buhunan shinkafa da wake 100,000 da dai sauransu.

Zulum ya ce hukumar NEC ta umarci hukumar NEMA ta raba kayan abinci ga iyakokin jihohin da jamhuriyar Nijar ta raba.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya ce ana ci gaba da duba rijistar jama’a.

Ya ce tuni Najeriya ta samu ‘yan gudun hijira daga jamhuriyar Nijar, lamarin da ya ce yana shafar rabon kayayyakin jin kai.

Sai dai gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya ce kawo yanzu an baiwa jihohi Naira biliyan biyu kacal maimakon Naira biliyan 5 da aka amince da su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button