Labarai
Da dumi’dumi: Shugaba Tinubu ya ba da umarnin biyan masu cin gajiyar NPower mutun dubu Dari hu’du 400,000.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin a gaggauta biyan kudaden alawus-alawus da ake bin Gwamnatin sa na masu cin gajiyar NPower a duk fadin kasar nan.
Umurnin Tinubu ya biyo bayan kammala wani atisayen tantancewa da ma’aikatar kula da jin kai da yaki da fatara ta tarayya ta kaddamar kuma ta kammala.
Umurnin shugaban da aka ce an samu a daren Laraba, ya jawo farin ciki daga masu cin gajiyar kimanin mutun 400,000 a fadin kasar.