Labarai

Da dumi’dumi: Shugaba Tinubu ya hana Karin ku’din Sukari tare da kokarin ragen farashin sakamakon watan azumi mai zuwa.

Spread the love

Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta hannun Ma’aikatar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, ta hada hannu da manyan kamfanoni a karkashin shirin farko na tsarin sarrafa sukari na kasa kan tsarin hadin gwiwa don dakile hauhawar farashin sikari da inganta karfin samar da sukari a cikin gida Najeriya wanda zai bayarda damar rage farashin.

Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Dr. Doris Uzoka Anite ne ya bayyana hakan bayan wani rangadin da ya kai kan kamfanonin sukari.

Ministan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ya ce an dauki matakin ne don kiyaye daidaiton farashin kayan masarufi, musamman a lokacin azumin Ramadan mai zuwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button