Labarai

Da dumi’dumi Tinubu ya amince da fitar da Bilyan 108bn domin tallafin Ambaliyar ruwa a jihar Borno da sauran su

Spread the love

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 108 domin tallafa wa jihohin kasar wajen magance bala’o’i, inda kowace jiha za ta karbi Naira biliyan 3 don taimakon kokarinsu.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, wanda a halin yanzu babban birninsa ke fama da matsananciyar ambaliyar ruwa sakamakon gazawar tashar ruwa ta Alau Dam, a jiya ya bayyana cewa ya karbi Naira biliyan 3 daga gwamnatin tarayya domin magance matsalar jin kai da ake fuskanta.

Da yake tabbatar da amincewar shugaban kasa kan asusun kula da bala’o’i, Shettima ya yi jawabi ga shugaban majalisar, inda ya ce: “Shugaban ya nuna himma da Jin kai da tausayi wajen hada hannu da jihohi wajen magance wadannan matsaloli.

“Kwanan nan, ya amince da a saki Naira biliyan 3 ga kowace jiha ta tarayya domin magance wasu kalubalen da ake fuskanta ta yadda dukkan sassan tarayya su samu saye da kuma mallakarsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button