Labarai

Da dumi’dumi: Tsofaffin alkalan Nageriya sun bukaci Kotun Koli ta tabbatar da Abba amatsayin Gwamnan jihar Kano domin domin Kotu da ma’aikatar shari’a su tsira da mutunci a idon duniya.

Spread the love

Gabanin zaman kotun koli da yanke hukunci kan karar zaben gwamnan jihar Kano da ake ta cece-kuce da shi, kungiyar ma’aikatan shari’a da suka yi ritaya a karkashin kungiyar ‘Transparent Justice Initiative’ sun bukaci kotun koli da ta tabbatar da abin da ta kira nasarar da gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf (Abba Gida Gida) ya samu) domin tsiran shari’a daga kara jin kunya.

A cewar kungiyar, bangaren shari’a ya kasance fata na karshe na talaka don haka ya kamata ta rika yin hakan a cikin hukunce-hukuncen ta musamman kan harkokin zabe.

“Muna cikin damuwa da hukuncin kotun daukaka kara da kuma kura-kurai da suka biyo baya a cikin jama’a, a matsayinmu na gungun ma’aikatan da suka yi ritaya, muna so mu tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kotun koli a matsayin mai shari’a ta karshe da kuma matakin karshe na warware takaddama za ta tabbatar da an yi adalci.

Idan ba a manta ba, kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta amince da hukuncin kotun da ta kori Gwamna Yusuf tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

A cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun kodinetan kungiyar Transparent Justice Initiative, Mista Stanley Kingsley, kuma aka rabawa manema labarai yau a Kaduna, kungiyar wadda ta bayyana amincewa da kotun kolin ta ce, “A tsawon shekarun da suka gabata ta nuna iya kare doka da oda don tabbatar da komar doka da kiyaye haƙƙin mutane.”

“Kuma ba mu da shakku a zukatanmu cewa kotun koli za ta yi nazari sosai kan shari’ar kotun da kuma hukuncin kotun daukaka kara domin tabbatar da cewa muryoyin jama’a da ‘yancinsu wadanda suke da matukar muhimmanci kuma an tabbatar da su kamar yadda kundin tsarin mulkinmu ya tanada a dokar zabe .”

Yayin da yake lura da cewa zai kai ga shari’ar “rashin adalci” ga kotu ta cire dan takarar da jama’a suka zaba. Mun ga yadda a ranar 18 ga Maris, 2023 jama’a suka fito gaba daya suka zabi Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuri’u 1,019,602 da tazarar kuri’u 128,897 tsakaninsa da dan takarar jam’iyyar APC na biyu.

Kwamitin ya tabbatar da hukuncin kotun da Mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ya jagoranta na korar Yusuf a ranar 20 ga watan Satumba, 2023. Karamar kotun ta bayyana kuri’u 165,663 na Yusuf wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) a matsayin mara inganci bisa dalilan da suka sa aka soke zaben. Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ba ta sanya hannu ko tambarin ba.

“Mun yi karatun ta nutsu kuma mun gano cewa wannan shi ne karo na farko a tarihi da wata kotu za ta soke zaben da aka yi kan rashin sanya hannu a bayan katin zabe kuma dole ne a kauce wa hakan nan gaba.

Kungiyar da ta bukaci kotun da ta yi watsi da matsin lamba daga bangaren shari’a ta ce, “Mun yi imani kuma muna da cikakken yakinin cewa kotun koli za ta yi abin da ya kamata tare da tabbatar da al’ummar Kano da suka kada kuri’a.

“A ko’ina a duniya ana mutunta bangaren shari’a da kuma dogaro da shi wajen tabbatar da adalci kuma mun yi imani da cewa hakan zai kasance.

Don haka ta bukaci ‘yan Najeriya da kada su daina amincewa da bangaren shari’a domin ya kasance cibiya ce mai dogaro da ke karfafa dimokuradiyya .

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button