Labarai
Da dumi’dumi: wani magidanci ya kashe Kansa Sakamakon kuncin rayuwar mulkin Tinubu a jihar Jigawa.
Rahotonni daga Jihar Jigawa na cewa Wani Mutum ya kashe Kansa ta Hanyar Rataye kansa wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa shedun kusa da bawan Allah sun tabbatar da cewa magidancin ya kashe Kansa ne Sakamakon tsadar rayuwa da kuma Kuncin Rayuwa da yake Fuskanta.
Wannan al’amari ya faru ne a ƙauyen Dungun Tantama Yankin Ruba A Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa Dake Jihar Jigawa a Arewacin Nageriya
Al’ummar Nageriya musamman talakawa na fuskantar matsin rayuwa tun bayan cire tallafin man fetir da Shugaba Bola Tinubu ya yi bayan ya karbi rantsuwar kama Aiki.