Labarai

Da dumi’dumi: ‘Yan bindiga sun kashe mutum talatin 30 a wani sabon harin da aka kai a jihar Filato

Spread the love

Akalla mutane 30 ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Kwahaslalek da ke karamar hukumar Mangu a jihar Filato da sanyin safiyar yau ranar Laraba a jihar Filato.

An tattaro cewa wadanda harin ya rutsa da su wadanda yawancinsu mata ne da kananan yara, sun garzaya gidan wani shugaban al’umma da ke yankin ne a daren ranar Talata domin tsira da rayukansu sakamakon wani rikici da ya barke da rana a garin Mangu inda ‘yan bindigar suka kewaye su tare da kashe dukkaninsu. su

Wani shugaban al’ummar yankin mai suna Mark Haruna ya tabbatarwa da jaridar PUNCH Online adadin wadanda suka mutu a garin Jos babban birnin jihar a ranar Larabar da ta gabata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button