Da dumi’dumi: ‘yan bindiga sun kashe mutun Goma a jos.
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a unguwar Kulben da ke karamar hukumar Mangu ta jihar Filato inda suka kashe mutane 10.
Wani mazaunin kauyen Kulben, Moses Fwan, a ranar Litinin ya tabbatarwa da jaridar The PUNCH da ke Jos harin.
Fwan ya ce lamarin da ya faru a daren Lahadin da ta gabata ya kuma yi sanadiyyar lalata gidaje da dama na mutanen kauyen da ‘yan bindigar suka lalata kafin su gudu daga cikin al’ummar.
Fwan ya ce, “Rundunar ‘yan bindigar Fulani ne suka kai hari a kauyen Kulben da ke gundumar Kombun a karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato.
‘Yan bindigan sun zo kauyen ne da misalin karfe 10:00 na dare ranar Lahadi 10/09/2023 suka kashe mutanenmu 10. Sun kuma raunata wasu da dama tare da lalata mana dukiyoyi da suka hada da gidaje.
A halin yanzu, mutanenmu suna alhinin kisan gillar da aka yi wa ‘yan uwansu, kuma ana ci gaba da shirye-shiryen gudanar da jana’izar jama’a ga wadanda aka kashe.”
Shugaban kungiyar ci gaban Mwaghavul a gundumar Kombun, Dokta Elisha, wanda shi ma ya tabbatar da harin ya ce, “Daga bayanan da na samu, an kashe mutane 10 a yayin farmakin. Ina kan hanyara ta zuwa ƙauye.”
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, Alfred Alabo, ya ce har yanzu ofishinsa bai samu rahoton faruwar lamarin ba.
Da aka tuntubi jami’in yada labarai na rundunar soji ta musamman mai kula da wanzar da zaman lafiya a jihar, Captain Oya James, ya ce bai san da faruwar lamarin ba.
James, ya yi alkawarin gudanar da bincike kan lamarin tare da daukar matakin da ya dace don dakile afkuwar lamarin.