Labarai

Da dumi’dumi: ‘yan bindiga sun kashe mutun hu’du sun Kuma sace mutun takwas a katsina.

Spread the love

Wasu mahara da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe manoma hudu tare da yin garkuwa da wasu mutane takwas daga kauyen Nahuta da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina a ranar Asabar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da faruwar harin ranar Lahadi a Katsina.

Ya ce manoman suna girbin amfanin gonakinsu ne lokacin da maharan suka kai farmaki.

Daya daga cikin manoman da suka yi nasarar tserewa ya samu raunukan harbin bindiga, ya kara da cewa.

‘Yan bindigar da ake zargin sun kai wa manoman hari, inda suka bude musu wuta inda suka kashe hudu tare da jikkata daya; sun kuma yi awon gaba da wasu takwas,’’ inji Aliyu. (NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button