Labarai

Da dumi’dumi: ‘yan bindiga sun kashe mutun Sha biyu a jihar Taraba.

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe manoma 10 daga gida daya a jihar Taraba a lokacin da suke shirin girbin amfanin gonakinsu.

Hakazalika, an kashe wasu makiyaya biyu a wani harin ramuwar gayya.

Daily Trust a yauranar Lahadin ta gano cewa an kai wa manoma hari ne a Jenuwa Gida da ke karamar hukumar Takum a jihar Taraba a ranar Juma’a.

An bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi wa manoman kwanton bauna a kusa da gonar su.

Shugaban kungiyar Kutep na kasa, Mista Emmanuel Ukwen, ya dora alhakin harin kan wasu da ake zargin makiyaya ne.

Ya yi zargin cewa, kwanaki kadan kafin kisan, an kashe wasu matasan Kutep biyu tare da yi wa wata mata fyade da wasu da ake zargin makiyaya ne suka yi, lamarin da ya tilasta wa matasan kai harin ramuwar gayya, wanda ya yi sanadin mutuwar makiyayan biyu.

Ukwen ya yi zargin cewa Fulani makiyaya sun kuma kai harin ramuwar gayya tare da kashe manoman Kutep 10.

Shugaban kungiyar Miyyetti-Allah shiyyar Kudancin Taraba, Ya’u Ibrahim Barewa, ya yi zargin cewa wasu Fulani makiyaya hudu da suka taso daga Takum zuwa Kashinbila, an kai masu gari wanda yake zargin matasan Kutep ne kan hanyarsu ta zuwa garin Kashinbila, inda aka kashe biyu, yayin da wasu biyu suka samu raunuka.

Ya kuma yi zargin cewa ‘yan Kutep sun kashe shanu 15, inda ya kara da cewa sun kai rahoto ga sashin ‘yan sanda na Takum.

Yau Ibrahim ya ce da wuya a ce a zahiri su waye ne suka kashe manoman Kutep 10 tunda ba a kama su ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan SP Usman Abdullahi ya tabbatar da cewa wasu da ba a san ko su wanene ba sun kashe manoman Kutep guda 10 a kewayen Jenuwa Gida a karamar hukumar Takum.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button