Labarai

Da dumi’dumi: ‘yan bindiga sun kashe mutun Tara 9 sun Kuma yi garkuwa da mutane da dama a danmusa dake Jihar katsina.

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga da yawansu ya kai sun kai farmaki garin Danmusa hedikwatar karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina, inda suka kashe mutane tara.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan bindigar sun kai hari garin ne da misalin karfe 8 na daren Lahadi, inda suka yi ta sama da fadi da su na tsawon sa’o’i, inda suka kashe mutum tara ciki har da dan sanda guda.

Ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutane har yanzu ba a tantance adadinsu ba tare da jikkata wasu da dama.

Ya kara da cewa maharan sun kai farmaki gida gida, inda suka yi awon gaba da wasu kayayyaki masu daraja.

A yayin da nake magana da ku, akwai jami’an tsaro da ke harbin bindiga,” inji shi.

Wata majiya a garin ta ce biyu daga cikin wadanda aka kashen makwabtan sa ne, inda ta kara da cewa dan sandan da aka kashe a lokacin da suka kai farmaki gida-gida bayan sun ga kakin sa ne.

“A halin yanzu muna shirye-shiryen gawarwakinsu don jana’izar,” in ji shi, ya kara da cewa kimanin mutane bakwai kuma an yi garkuwa da su.

Wasu majiyoyi da ba a tabbatar da su ba a cikin al’ummar yankin sun ce mai yiwuwa maharan na cikin wani shiri ne na ramuwar gayya, kasancewar daya daga cikin jagororin ‘yan ta’addan ne suka kama tare da kashe shi a hannun sabbin jami’an sa-ido a karamar hukumar.

“Akwai wani sarkin ‘yan fashi da ke kusa da kauyen Katsira wanda ya yi alfahari da cewa zai kawar da sabbin jami’an sa ido na al’umma. Nan dai suka hada kai suka kashe shi.

“Bayan kwanaki kadan ne, kuma shi ya sa muka yi imani da cewa ‘ya’yansa sun hada kai don kai harin,” in ji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, wanda ya tabbatar da harin na daren jiya, ya ce an kashe mutane biyar.

Ya yi alkawarin komawa ga wakilinmu domin jin karin bayani kan lamarin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button