da dumi’dumi ‘yan bindiga sun kashe Soja tare da sace kishiyar mahaifiyarsa a jihar Kaduna
Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari a kauyen Anguwan Rimi da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna, inda rahotanni suka ce sun kashe wani soja tare da sace mahaifiyarsa.
Ko da yake ‘yan sanda ba su mayar da martani kan lamarin ba; Wani dan yankin mai suna Mista Solomon, ya shaida wa manema labarai cewa, sojan da ya tashi daga Legas a ranar Lahadi yana tattaunawa da ‘yan uwa lokacin da ‘yan ta’addan suka mamaye gidan.
Ya ce “Lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, da misalin karfe 11:00 na rana, inda ‘yan bindigar dauke da bindigogi kirar AK-47 suka shiga gidan domin su yi awon gaba da uwar gidan, amma sojan ya yi turjiya.
‘Yan bindigar sun lura da kakin sa a rataye hakan yasa basuyi wata wata ba suka yi harbi ba tare da bata lokaci ba,” inji shi.
Ya ce al’umma sun shiga cikin tsoro da rudani, inda ya yi kira ga jami’an tsaro da su kubutar da uwar gidan tare da kamo ‘yan ta’addan.