Da dumi’dumi: ‘Yan bindiga sun sace mutun 25 sun kashe mutun daya a jihar Kaduna.

‘Yan bindiga sun kashe wani manomi tare da raunata biyu tare da yin garkuwa da wasu Mutane 25 a Ungwan Baka, Ward Agunu, a karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.
Duk da dai har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta mayar da martani kan lamarin ba, amma an shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar garin da bindigu da adduna da sanyin safiyar jiya, yayin da mutanen yankin ke barci.
Wani da ya tsira da ransa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce: “An yi garkuwa da mutane kusan 25 a Unguwan Baka da ke gundumar Agunu da sanyin safiyar Talata. Mutane biyu sun jikkata sannan mutum daya ya mutu.
“Mun garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti, muna yi musu fatan samun sauki da wadanda aka yi garkuwa da su, muna addu’ar Allah ya dawo da su lafiya. Don Allah a yi mana addu’a. Wannan shi ne hari na uku da ake kai wa al’ummarmu,” inji shi.