Labarai

Da dumi’dumi: ‘Yan bindiga sun sace mutun Goma 10 ciki harda mai Jego sabuwar haihuwa a jihar Zamfara.

Spread the love

‘Yan bindigar sun mamaye garin Zurmi ne da yammacin ranar Talata inda suka rika harbe-harbe, lamarin da ya tilastawa mazauna garin yin gudu domin tsira da rayukansu.

Dakarun Operation Hadarin Daji da aka tura garin sun yi artabu da ‘yan ta’addan a wani mummunan artabu da ya dauki tsawon sa’o’i da dama.

Wani mazaunin yankin mai suna Abubakar Zurmi ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa an yi garkuwa da mutane 10 a harin da suka hada da wata uwa mai shayarwa da jaririn da ta haifa.

“Yan ta’addan da yawansu ya shigo garin ne da misalin karfe 5:30 na yamma daga wurare daban-daban kuma suka fara harbin mutanen garin. Sojoji sun yi iya kokarinsu wajen dakile harin. Soja daya ya samu rauni a yayin harbin,” in ji Zurmi.

Ya kara da cewa “har ya zuwa yanzu kimanin mutane 10 ne suka bata wadanda muka yi imanin an yi garkuwa da su, ciki har da wata uwa mai shayarwa da ta haihu kimanin mako guda da ya wuce.”

Hukumomin ‘yan sanda a jihar dai ba su ce uffan ba game da sabon harin da aka kai har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button