Labarai

Da dumi’dumi: ‘Yan bindiga sun sace Shugaban Karamar Hukumar akwanga dake jihar Nasarawa.

Spread the love

‘Yan bindiga dai na ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankin Arewa ta Tsakiya da kuma Arewa maso Yamma na kasar nan duk da cewa akwai jami’an tsaro.

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa, Safiyanu Isa Andaha.

Jami’an ‘yan sanda sun ce, an sace Shugaban Karamar Hukumar ne a daren ranar sabuwar shekara a kauyen Ningo da ke kan titin Andaha – Akwanga, tare da wani dan asalin yankin.

A cewar jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, Ramhan Nansel, jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sauran hukumomi sun fara bin diddigin wadanda suka yi garkuwa da su cikin gaggawa domin ganin an sako mutanen.

Jihar Nasarawa dai kamar Zamfara na daya daga cikin jihohi da dama a yankin arewa maso yammacin Najeriya da tsakiyar Najeriya da ake fama da ta’addanci da ‘yan bindiga ke kai farmaki kauyuka da kashe mutane da sace mutane tare da kona gidaje bayan sun yi awon gaba da su.

’Yan bindigar na rike da sansanoni ne a wani katon dajin da ya ratsa jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da Neja.

Kasar dai na fuskantar dimbin kalubalen tsaro da suka hada da rikicin jihadi na tsawon shekaru 14 a yankin arewa maso gabas wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 40,000 tare da tilasta wasu fiye da miliyan biyu barin gidajensu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button