Da dumi’dumi: ‘Yan bindiga sun sace ‘yan mata daliban Jami’ar Al-qalam dake jihar Katsina.
Masu garkuwa da mutane sun sace ɗalibai mata su 2 a jami’ar Al-Qalam dake jihar Katsina.
Katsina Post ta ruwaito cewa, waɗanda lamarin ya rutsa da su, sun haɗa da Habiba Ango Shantali, da kuma Maryam Abubakar Musa, waɗanda dukkan su ‘yan asalin jihar Neja ne.
Lamarin ya faru ne yayin da ɗaliban ke kan hanyar su ta dawowa makarantar a
ranar Litinin, 15 ga watan Janairu na shekarar 2024.
Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Jihar Neja (NANISS) na ƙasa, Kwamared Gambo Idris Shehu, shi ne ya tabbatar da sace ɗaliban a wata sanarwa da Sakatare-janar na ƙungiyar, Kwamared Mohammed Ibrahim ya fitar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Mun samu labarin sace wasu ɗalibanmu biyu na jihar Neja da ke karatu a Jami’ar Al-Qalam a jibar Katsina a kan hanyarsu ta komawa makaranta”.