Labarai

Da dumi’dumi: ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wata mata da jaririnta dan wata shida da wasu ‘ya ‘yanta biyu a birnin tarayya Abuja.

Spread the love

An bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 8 na dare zuwa karfe 9 na yammacin ranar Lahadi, inda suka rika harbi ba kakkautawa.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu Gungun mutane dauke da muggan makamai da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi awon gaba da wata mata da jaririnta dan watanni shida da kuma wasu ‘ya’yanta biyu a yankin shiyya ta 5 da ke rukunin kaura na Kubwa Extension 2 da ke kan titin Arabiya a babban birnin tarayya.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa jaridar PUNCH cewa garkuwa da mutane ya zama ruwan dare gama gari a yankin duk watan Disamba.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa, “Wannan garkuwar na faruwa ne saboda rashin isasshen tsaro a yankin. A daren jiya sun yi garkuwa da iyali baki daya – wata uwa da ‘ya’yanta uku, ciki har da wani jariri dan wata shida a nan shiyya ta 5, Kubwa Extension 2 Relocation estate.”

Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ba ta ce uffan a hukumance dangane da faruwar lamarin ba.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, da aka tuntube shi a yau ranar Litini, ya yi alkawarin jin yadda lamarin ya faru zai Kuma sanar daga baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button