Labarai

Da dumi’dumi: ‘Yan boko Haram sun kashe babban limanin garin Beneshiekh dake jihar Borno.

Spread the love

A jiya ne wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’addan Boko Haram ne, sun kai farmaki garin Beneshiekh hedikwatar karamar hukumar Kaga a jihar Borno, inda suka kashe babban limamin Garin Sheihk Baba Goni Muktar Malumti.

Sun kuma kona wasu littafan addinin musulunci na marigayin.

Marigayin fitaccen malamin addinin musulunci ne kuma babban limamin masallacin Juma’a, Beneshiekh.
Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da wasu gungun ‘yan ta’adda suka mamaye kauyen Makinta Kururi na Beneshiekh inda suka yi awon gaba da mafarauta biyu a wani sabon hari da suka sake kai musu.

Idan ba a manta ba a watan da ya gabata ne mahara suka kashe kanin babban Limamin.

Beneshiekh dake kan babbar hanyar Kano zuwa Damaturu zuwa Maiduguri, yana da nisan kilomita 70 zuwa Maiduguri.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban riko na karamar hukumar Kaga, Mustapha Baima, ya bayyana kaduwarsa kan sabbin hare-haren da ‘yan ta’addan ke kaiwa inda ya ce, “Eh mun samu labarin cewa ‘yan Boko Haram sun bindige babban limamin masallacin Juma’a na Beneshiekh a gidansa da misalin karfe uku na safe. 1:15 na safe ranar Litinin.

“’Yan ta’addan sun fara kai farmaki gidan wani Malamin addinin Musulunci (an sakaya sunansa), amma da suka fahimci hoton da suke dauke da shi domin aiwatar da hukuncin kisa bai yi kama da na babban Limamin da suka zo kashewa ba, sai suka ce ya koma gidan ya ci gaba da zama. .

Daga nan suka je wani gida inda babban Limamin yake Sallah. Daga nan ne ‘yan ta’addan suka bude wuta kan samun inda suka kai hari. ‘Yan ta’addan sun kuma kona wasu Littattafan Musulunci bayan sun kashe babban Limamin.

Wasu ‘yan ta’addan kuma sun mamaye Makinta Kururi inda suka yi awon gaba da mafarauta biyu. Wannan baya ga kashe wani kanin marigayi babban Limamin.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button