Labarai

Da dumi’dumi: ‘Yan Boko Haram sun kashe matasa mutun Sha bakwai 17 A Geidam dake jihar Yobe.

Spread the love

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe wasu matasa 17 a kauyen Gurokaya da ke karamar hukumar Geidam a jihar Yobe, sakamakon rashin biyan haraji.

Daily Trust ta ruwaito labarin cewa ‘yan ta’addan sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 10 na daren ranar Litinin, inda suka tattaro mazauna wuri guda tare da aiwatar da kashe-kashe.

“Sun zabo matasa 21 da ke tsakanin shekaru 20 zuwa 30, suka harbe su a kusa, yayin da kananan yara da tsofaffi suka tsira.

“Mutane 17 ne suka mutu nan take, yayin da sauran hudun kuma aka garzaya da su asibiti cikin mawuyacin hali,” kamar yadda wata majiyar tsaro ta shaida wa wakilinmu.

Ya ce maharan sun dauki matakin ne bayan gargadi da aka yi wa mutanen kauyen da su biya haraji amma abin ya ci tura.

“Bayan wannan danyen aikin, sun sake yin wani gargadi ga mutanen kauyen kan sakamakon kaucewa biyan haraji kafin su tafi,” in ji shi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babagana Aisami Geidam wani mai fafutukar kare hakkin bil’adama ya shaida wa wannan jarida cewa an binne gawarwaki 16 kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Ya ce an tura jami’an soji zuwa kauyen da abin ya shafa.

Da aka tuntubi mataimakin daraktan hulda da jama’a na Operation Lafiya Dole, Captain Muhammad Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun kuma yi zargin cewa an bai wa mutanen kauyen bayanai ga sojojin da suke fatattake su daga maboyarsu.

“Su (’yan ta’adda) sun kai wa mutanen kauyen hari ne a matsayin ramuwar gayya saboda zargin cewa suna taimaka mana da bayanai masu amfani don fatattakar su.

“Ba zan iya ba ku cikakken adadin wadanda suka mutu ba, amma abin da na sani shi ne an tura jami’an soji kuma an dawo da zaman lafiya,” in ji shi.

Mazauna garin Geidam sun koka matuka dangane da yadda ‘yan tada kayar bayan ke yi a wajen garin ba tare da daukar matakan da suka dace ba.

A makon da ya gabata, maharan sun kai hari wani gidan kwastam da ke tsakiyar garin Geidam inda suka kashe wani jami’in rundunar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button