Labarai

Da dumi’dumi: ‘Yan Daba na sace mana kayayyakin zabe a Jihohin Enugu da Kano a zaben cike Gurbi ~Hukumar Zaben INEC.

Spread the love

Hukumar Zabe INEC ta bayyana a shafinta na facebook tana Mai cewa an buɗe rumfunan jefa ƙuri’an cike Gurbi kuma ana gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali a runfunan jefa ƙuri’a 8,934 a cikin Jihohi 26 da aka gudanar da zaɓen a yau.

Duk da haka, muna sa ido kan yadda ayyukan ‘yan daba da sace-sacen kayayyaki ke faruwa a wasu wurare a jihohin Akwa Ibom, Enugu da Kano.

A mazabar tarayya ta Ikono/Ini dake jihar Akwa Ibom, muna gudanar da bincike kan lamarin da ya faru a Hall Hall, EdemUrua 003 a karamar hukumar Ini da kuma Hall Hall Mbiabong Ikot Udo 003 a karamar hukumar Ikono.

A mazabar Enugu ta Kudu 1 a jihar Enugu, muna gudanar da bincike kan rahotannin tarzoma a rumfunan zabe 8 da ke Uwani West Ward.

A mazabar Kunchi/Tsanyawa ta jihar Kano, an samu cikas a harkokin gudanar da zabe a karamar hukumar Kunchi da suka hada da rumfunan zabe 10.

Za mu ci gaba da samar da jawabi akai-akai kan halin da ake ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button